Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Haramta giya ya sauka ne kuma ana yin ta daga abubuwa biyar ne: inibi, dabino, zuma, alkam…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن عَبْدُ الله بن عمر رضي الله عنهما أن عمر قال -على منبر رسول الله- صلى الله عليه وسلم : "أما بعد، أيها الناس، إنه نزل تحريم الخمر وهي من خمسة: مِنَ العنب، والتمر، والعسل، والحنطة، والشعير. والخمر: مَا خَامَرَ العَقْلَ. ثَلاثٌ وَدِدْتُ أَنَّ رَسُولَ الله صلى الله عليه وسلم كَانَ عَهِدَ إلَيْنَا فِيهَا عَهْداً نَنْتَهِي إلَيْهِ: الجَدُّ، والكَلالَةُ، وأَبْوَابٌ مِنَ الرِّبَا".
Umar Dan Khaddab -Allah ya yarda da shi- ya yi huduba a masallaci Manzon Allah -tsira da aminci su tabbata a gare shi- kuma akan minbarinsa, kuma ya tabbatar da cewa lallai giya itaa ce duk wani abu da zai iya jirkita hankali, ba wacce aka yi da inibi ba kawai, duk wani abin sha wanda zai iyi jirkita hankali ko da kuwa da dabino ko zuma ko alkama to suma sun zama giya, kuma hakika Uma r ya fadi abubuwa uku a cikin Hudubarsa wanda akawai rikitarwa a cikinsa kuma yayi burin ace Annabi yana raye, cikim wadan nan abubuwa guda uka da ya da aka kure matuka izuwa gare shi sune Gadon Kaka, da Gadon Mamacin da bashi da Da ko Mahaifi, da wasu abubuwa kan Riba, kuma Alhamdulillah cewa lallai Hukuncin wannan abubuwa guda uku sananne ne, kuma wannan ba yana nufin cewa Annabi baiyi bayaninsu ba Hakika Annabi ya Isar da Sakonsa, kuma ya bada Amana, kuma ya isar da sakon Allah abun da yafi wannan ma buya da kuma wanda ya fi wannan ma girma kuma Umar yana son yakasance akawai nassi gwari gwari ne a kansu da baya bukatar wani Ijtihadi.
Rukunan : HADDODI · HADDIN GIYA · LADUBBA NA SHARI'A · LADUBBAN CI DA SHA · FIƘHU DA USULU · FALALOLI DA LADUBBA