Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Mutane da yawa su cika Mutane, amma daga cikin Mata babu waxanda suka cika sai Asiya Matar…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 2عن أبي موسى رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «كَمُل من الرجال كثير، ولم يَكمُل من النساء: إلا آسية امرأة فرعون، ومريم بنت عِمران، وإنَّ فضلَ عائشة على النساء كفضل الثَّرِيد على سائر الطعام».
Lallai waxanda suka kai Matsayin cika a cikin Falalar Addini da Halayya daga cikin Maza akwai da yawa daga cikinsu akwai wanda yakai Matakin cika ta Al-ada Kamar Malamai da Mutanen kirki da Waliyyai, akwai daga cikin su akwai wanda ya wuce matakin cika kamar Annabwa, amma Matan da suka cika su ne kaxan kwarai kuma waxanda suke gaba Asiya Matar Fir'auna ita Asiya Bint Muzahim wacce Allah ya buga Misali da ita a cikin cikar Imani, sai ya ce: "Kuma Allah ya buga Misali ga waxanda sukai Imani Matar fir'auna" Saboda tayi Imani da Annabi Musa lokacin da yai Nasara kan Masu Sihirin fir'auna, kuma yayin da fir'auna ya san ta yi Imani sai yayi mata Azaba Mai tsanani har zuwa lokacin da ta Mutu tana riqe da Imaninta, amma ta biyu ita ce Maryam Bint Imran wacce Allah ya buga Misali wajen kare kanta, da kuma cikar Ibadarta, sannan SAW ya ce: "Kuma falalar Aisha kan sauran Mata kamar fifikon Tharid kan sauran Abinci" Tharid shi ne mafi daxin abincin Larabawa kuma anayinsa ne da gurasa da kuma nama, to Aisha a Fifikon ta kan Mata kamar Fifikon wancan Tharid xin wanda shi ne mafi daxin abinci kan Sauran Abinci
Rukunan : FALALAR IYAYEN MUMINAI · ILIMIN AƘIDA · SIRAR ANNABI · MATAYENSA TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARESHI DA YANAYIN GIDAN ANNABTA · IYALAN GIDAN ANNABI · SIRA DA TARIHI