Abubuwa guda huɗu wanda ya kasance a cikinsa to ya zama munafiki tsantsa, wanda ya kasance…

Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Abubuwa guda huɗu wanda ya kasance a cikinsa to ya zama munafiki tsantsa, wanda ya kasance…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Abubuwa guda huɗu wanda ya kasance a cikinsa to ya zama…

عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرٍو رضي الله عنهما قال: قال رَسولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَرْبَعٌ مَنْ كُنَّ فِيهِ كَانَ مُنَافِقًا خَالِصًا، وَمَنْ كَانَتْ فِيهِ خَلَّةٌ مِنْهُنَّ كَانَتْ فِيهِ خَلَّةٌ مِنْ نِفَاقٍ حَتَّى يَدَعَهَا: إِذَا حَدَّثَ كَذَبَ، وَإِذَا عَاهَدَ غَدَرَ، وَإِذَا وَعَدَ أَخْلَفَ، وَإِذَا خَاصَمَ فَجَرَ».

Bayanin hadisin: Abubuwa guda huɗu wanda ya kasance a cikinsa to ya zama…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi daga ɗabi'u huɗu idan sun taru a tare da musulmi to ya zama mai tsananin kama da munafukai saboda waɗannan ɗabi'un, wannan ga wanda galibi suka zama a tare da shi akwai waɗannan ɗabi'un, amma wanda suka zama kaɗan to bai shiga cikin su ba, sune:

Na farko: Idan zai yi zance sai ya yi gangancin ƙarya da rashin gaskiya a cikin zancensa.

Na biyu: Idan aka yi yarjejeniya da shi ba zai cika ba, kuma ya yaudari abokinsa.

Na uku: Idan ya yi alƙawari ba zai cika shi ba kuma sai ya saɓa shi.

Na huɗu: Idan aka yi faɗa da shi kuma ya yi rigima tare da wani sai husumarsa ta zama mai tsanani, kuma ya bauɗe daga gaskiya, ya yi dabarar a kin karbar gaskiya da ɓata ta, kuma ya faɗi ɓata da ƙarya.

Domin munafunci shi ne bayyanar da sabanin abinda aka ɓoye, wannan ma'anar samammiya ce a tare da mai waɗannan ɗabi'un, kuma munafuncinsa ya zama a cikin haƙƙin wanda ya zantar da shi, kuma ya yi masa alƙawari, ya amince masa, ya yi husuma da shi, ya yi yarjejeniya da shi cikin mutane, ba wai cewa shi munafuki ne a cikin musulunci ba sai ya bayyanar da shi alhali shi yana ɓoye kafirci, wanda ya kasance a cikinsa akwai wata ɗabi'a daga waɗannan ɗabi'un; to a cikinsa akwai siffa ta munafunci har sai ya barta.

Koyarwar hadisin: Abubuwa guda huɗu wanda ya kasance a cikinsa to ya zama…

Rukunan : LADUBBA NA SHARI'A · ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI · LADUBBAN MAGANA DA SHIRU · ILIMIN AƘIDA · ZARGIN AYYUKAN SAƁO · FALALOLI DA LADUBBA · ABUBUWAN DA AKA HANA FURTAWA DA ILLOLIN HARSHE · SUNAYE DA HUKUNCE-HUKUNCE · MUNAFUNCI

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
لا إله إلا الله Babu abin bautawa sai Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah