Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > An gina Musulunci abisa abubuwa biyar
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 2عَنْ عَبْدِ اللهِ بنِ عُمَر رضي الله عنهما قال: قال رسولُ الله صلى الله عليه وسلم: «بُنِيَ الْإِسْلَامُ عَلَى خَمْسٍ: شَهَادَةِ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، وَأَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ، وَإِقَامِ الصَّلَاةِ، وَإِيتَاءِ الزَّكَاةِ، وَحَجِّ الْبَيْتِ، وَصَوْمِ رَمَضَانَ».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kamanta musulunci da ingantaccen gini da rukunansa biyar masu dauke da wancan ginin, ragowar dabi'un musulunci kamar cika ginin ne, Farkon wadanan rukunan: Shaidawa biyu; shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, (shaidawa) Annabi Muhammadu Manzon Allah ne, su rukuni daya ne; dayansu ba ya rabuwa da dayan, bawa zai furtasu yana mai tabbatar da kadaituwar Allah da kuma cancantarSa ga bauta Shi kadai banda waninSa, kuma yana mai aiki da abinda suka hukunta, kuma yana mai imani da Manzancin Annabi Mukammadu - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana mai binsa. Rukuni na biyu: Tsaida sallah, su ne sallolin farillai biyar a yini da dare: Asuba, da Azahar, da La'asar, da magariba, da Lisha, da sharuddansu da rukunansu da wajibansu. Rukuni na uku: Fitar da zakkar farilla, ita ibada ce ta dukiya wajiba a kowacce dukiyar da takai wani gwargwado abin iyakancewa a shari'a, ana bada ita ga wadanda suka cancanceta. Rukuni na hudu: Hajji, shi ne nufin Makka dan tsaida ibadu, dan yin bauta ga Allah - Mai girma da daukaka -. Rukuni na biyar: Azumin Ramadan, shi ne kamewa daga ci da sha da wasunsu daga masu bata azimi da niyyar bauta ga Allah, daga bullowar alfijir zuwa faduwar rana.
Rukunan : FIƘHU NA IBADA · SALLAH · ZAKKA · AZUMI · HAJJI DA UMRA · ILIMIN AƘIDA · FIƘHU DA USULU · WAJIBCIN SALLAH DA HUKUNCIN MAI BARINTA · WAJIBCIN ZAKKKA DA HUKUNCIN MAI ƘIN BAYARWA · Obligation of Fasting and Ruling of Its Abandoning · Obligation of Hajj and ‘Umrah and Ruling of Its Abandoner · IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA · Imani da Manzanni · SUNAYE DA HUKUNCE-HUKUNCE · ANNABTA · MUSULUNCI