Shin ba zan baku labarin 'yan aljanna ba? Duk mai rauni da ake rainawa, da zai rantse da A…

Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Shin ba zan baku labarin 'yan aljanna ba? Duk mai rauni da ake rainawa, da zai rantse da A…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Shin ba zan baku labarin 'yan aljanna ba? Duk mai rauni…

Bayanin hadisin: Shin ba zan baku labarin 'yan aljanna ba? Duk mai rauni…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin sashin siffofin 'yan aljanna da 'yan wuta.

Mafi yawancin 'yan aljanna sune: "Dukkan mai rauni mai ƙanƙar da kai", wato: Mai ƙanƙan da kai mai ƙanƙanr da kai ga Allah - Maɗaukakin sarki -, mai ƙasƙantar da kansa gareShi, har takai wasu daga mutane suna raunana shi kuma suna wulaƙanta shi, wannan mai ƙasƙantar da kai ga Allah - Maɗaukakin sarki - da zai yi rantsuwa da Allah dan kwaɗayi a cikin karamcin Allah - Maɗaukakin sarki -, da Allah Ya kuɓutar da shi, kuma Ya tabbatar masa da abinda ya yi rantsuwa akansa kuma Ya amsa buƙatarsa da addu'arsa.

Kuma mafi yawancin 'yan wuta su ne: Dukkan "Mai ƙaton ciki" shi ne mai kaushin zuciya, mai bushewar zuciya mai tsananin husuma, ko mai alfasha wanda ba ya jawuwa ga alheri, "Mai yawan girman kai" shi ne mai girman kai, mai yawan ci, mai ƙiba, mai taƙama a tafiyarsa, mai mummunar ɗabi'a, "Mai girman kai" saboda butulcewarsa ga gaskiya, da kuma wulaƙanta waninsa.

Koyarwar hadisin: Shin ba zan baku labarin 'yan aljanna ba? Duk mai rauni…

Rukunan : ILIMIN AƘIDA · Imani da Ranar Lahira · RAYUWAR LAHIRA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
لا حول ولا قوة إلا بالله Babu wata ƙarfi ko iko sai na Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah