Idan zaku roƙi Allah to ku roƙe shi Firdausi
Musulunci > Ha > Hadith > Fihun adduoi da zikirai > Idan zaku roƙi Allah to ku roƙe shi Firdausi
Wanda ya ruwaito hadisin: Tirmizi ne ya ruwaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Idan zaku roƙi Allah to ku roƙe shi Firdausi
Bayanin hadisin: Idan zaku roƙi Allah to ku roƙe shi Firdausi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa a cikin aljannar Lahira akwai darajoji da matsayi ɗari, tsakanin kowace daraja a nisa kamar tsakanin sama da ƙasa ne, kuma mafi ɗaukakar waɗanan aljannatan ita ce aljannar Firdausi, daga nan ne ƙoramun aljanna huɗu suke ɓuɓugowa, a saman Firdausi ne al’Arshi yake; idan zaku roƙi Allah to ku roƙe Shi Firdaus; saboda ita ce a saman dukkaninl aljannatan.
Koyarwar hadisin: Idan zaku roƙi Allah to ku roƙe shi Firdausi
- Fifikon 'yan aljanna a matsayinsu, hakan kuma gwargwadan imani da ayyuka na gari.
- Kwaɗaitarwa akan roƙon Allah Firdausi maɗaukakiya daga gidajan aljanna.
- Firdausi ita ce mafi ɗaukakar gidajan aljanna, kuma mafificinsu.
- Yana kamata ga musulmi himmarsa ta zama maɗaukakiya, kuma ya yi ƙoƙari ya nemi mafi ɗaukakar matsayai kuma mafifitansu a wurin Allah - Maɗaukakin sarki -.
- Ƙoramun aljanna huɗu su ne ƙoramun ruwa da nono da giya da zuma waɗanda aka ambata a ciki AlƘur'ani a cikin faɗinSa - Maɗaukakin sarki -; {Kwatankwacin aljannar da aka yi wa masu tsoron Allah alƙawari a cikinta akwai ƙoramu na ruwa ba mai sakewa ba, da ƙoramu na nonon da ɗanɗanonsa bai canja ba, da ƙoramu na giya masu ɗaɗi ga masu sha da ƙoramai na tatacciyar zuma} [Muhammad: 15].
Rukunan :
FIƘHUN ADDU'O'I DA ZIKIRAI
· ILIMIN AƘIDA
· ADDU'O'I DA AKA RUWAITO
· FALALOLI DA LADUBBA
· Imani da Ranar Lahira
· RAYUWAR LAHIRA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
سبحان الله وبحمده
Tsarkin Allah da godiyarSa