Musulunci > Ha > Hadith > Sira da tarihi > To, ɗabi’un Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sun kasance Alƙur’ani ne
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1قال سعد بن هشام بن عامر -عندما دخل على عائشة رضي الله عنها-: يَا أُمَّ الْمُؤْمِنِينَ، أَنْبِئِينِي عَنْ خُلُقِ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَتْ: أَلَسْتَ تَقْرَأُ الْقُرْآنَ؟ قُلْتُ: بَلَى، قَالَتْ: فَإِنَّ خُلُقَ نَبِيِّ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ الْقُرْآنَ.
An tambayi Uwar Muminai A'isha Allah Ya yarda da ita, a kan ɗabi’un Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sai ta amsa, da jawabi gamamme, ta kuma mayar da mai tambayar zuwa Alƙur’ani mai girma wanda ya ƙunshi dukkanin siffofi na kamala, sai ta ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana ɗabia’antuwa ne da ɗabi’u na Alƙur’ani, abin da Alƙur’ani ya yi umarni ya yi, kuma abin da Alƙur’ani ya hana ya nisance shi, sai ɗabi’unsa suka kasance aiki da shi da tsayawa inda ya iyakance, da ladabtuwa da ladubansa da ɗaukar izina da misalai da ƙissoshinsa.
Rukunan : SIRAR ANNABI · ƊABI'U IRIN NA (ANNABI) MUHAMMAD · SIFFOFINSA NA HALITTA · SIRA DA TARIHI