Shimfiɗar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance ta jemam…
Musulunci > Ha > Hadith > Abubuwa masu tausasa zukata da waazozi > Shimfiɗar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance ta jemam…
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Shimfiɗar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabb…
Bayanin hadisin: Shimfiɗar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabb…
Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa shimfiɗar da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake kwanciya a kanta ta kasance an yi ta ne da jemammiyar fata, kuma a cike ta ke da kaba ta dabino, haka ma matashinsa wanda yake kishingiɗa a kansa.
Koyarwar hadisin: Shimfiɗar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabb…
- Bayanin abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake a kansa na zuhudu da bijirewa jin daɗin duniya, tare da cewa Allah - tsarki ya tabbatara maSa Ya ɗaukaka - Ya tabbatar masa da hakan inda a ce ya so ya ji daɗin da ita.
- Halaccin mallakar shimfiɗa da matashi, da kuma bacci a kansu dan jin sauƙaƙa yin bacci.
- Yana kamata ga musulmi ya lura da halinsa da kuma rayuwarsa da halin Annabinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, domin cewa shine abin koyi mai kyau, kuma wanda ya bi tafarkinsa ya shiriya kuma ya rabauta a duniya da lahira.
- Kwaɗayi akan yin tanadi domin lahira, kuma mumini ya wadatu da abin da zai taimake shi akan biyayya ga Allah a duniya, kuma kada ya shagalta da neman tara dukiya a duniya, haƙiƙa Allah Ya zargi wasu mutane sai ya ce: {Alfahari (da yawan 'ya'ya da dukiya) ya shagaltar da ku. Har (kuka mutu) kuka ziyarci ƙaburbura} [al-Takasur: 1-2].
Rukunan :
ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI
· ZARGIN SON DUNIYA
· SIRAR ANNABI
· ƊABI'U IRIN NA (ANNABI) MUHAMMAD
· FALALOLI DA LADUBBA
· TSARIN ANNABI
· SIRA DA TARIHI
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
الله أكبر
Allah Shi ne Mafi Girma