Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Ka guji duniya sai Allah Ya so ka, ka guji abin da ke hannun mutane sai mutane su so ka
Nawawi ya ce: Hadisi ne mai kyauAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عَنْ أَبِي العَبَّاسِ سَهْلِ بْنِ سَعِدٍ السَّاعِدِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: جَاءَ رَجُلٌ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، دُلَّنِي عَلَى عَمَلٍ إِذَا عَمِلْتُهُ أَحَبَّنِي اللَّهُ وَأَحَبَّنِي النَّاسُ، فَقَالَ: «ازْهَدْ فِي الدُّنْيَا يُحِبُّكَ اللَّهُ، وَازْهَدْ فِيمَا عِنْدَ النَّاسِ يُحِبُّكَ النَّاسُ».
Wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da shi zuwa aikin da idan ya aikata shi Allah zai so shi kuma mutane ma zasu so shi, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Allah zai so ka idan ka bar mafifici a duniya, da abin da ba zai amfaneka a lahira ba, kuma ka bar abin da zai iya yi wuwa a cikinsa akwai cutarwa a Addinika, kuma mutane zasu so ka idan ka guji abinda ke hannunsu na duniya; domin su a ɗabi'arsu suna sonta, wanda kuwa ya yi gogayya da su a kanta zasuƙi shi, wanda ya bar musu ita zasu so shi.
Rukunan : ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI · ZUHUDU DA TSANTSENI · FALALOLI DA LADUBBA