Shin ba na ba ku labarin mafi girman zunubai ba?

Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Shin ba na ba ku labarin mafi girman zunubai ba?

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Shin ba na ba ku labarin mafi girman zunubai ba?

عن أبي بكرة رضي الله عنه قال: قال النبي صلى الله عليه وسلم: «‌أَلَا ‌أُنَبِّئُكُمْ بِأَكْبَرِ الْكَبَائِرِ؟» ثَلَاثًا، قَالُوا: بَلَى يَا رَسُولَ اللهِ، قَالَ: «الْإِشْرَاكُ بِاللهِ، وَعُقُوقُ الْوَالِدَيْنِ» وَجَلَسَ وَكَانَ مُتَّكِئًا، فَقَالَ: «أَلَا وَقَوْلُ الزُّورِ»، قَالَ: فَمَا زَالَ يُكَرِّرُهَا حَتَّى قُلْنَا: لَيْتَهُ سَكَتَ.

Bayanin hadisin: Shin ba na ba ku labarin mafi girman zunubai ba?

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba wa sahabbansa labari game da mafi girman zunubai, sai ya ambaci waɗannan ukun:

1. Yi wa Allah shirka: Shi ne juyar da kowanne nau'in ibada ga wanin Allah, da daidaita wanin Allah da Allah a AllantakarSa da UbangidantakarSa da sunayenSa da siffofinSa.

2. Saɓawa iyaye: Shi ne kowacce irin cutarwa ga iyayen, magana ce ko aiki, da barin kyautatawa musu.

3. Faɗin zur, shaidar zur tana daga ciki: Shi ne dukkanin maganar da take ƙarya ce da aka yi nufin tauye wanda ta faɗa kansa ta hanyar ƙwace dukiyarsa da keta mutuncinsa, ko makamancin hakan.

Haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya maimaita gargaɗi game da faɗin zur don faɗakarwa a kan muninta da mummunan gurbinta ga zamntakewa, har sai da sahabbansa suka ce: Ina ma dai ya yi shiru don tausaya masa, da kuma ƙin abin da zai tayar masa da hankali.

Koyarwar hadisin: Shin ba na ba ku labarin mafi girman zunubai ba?

Rukunan : FIƘHUN HALAYE · ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI · HALAYE ABIN ZARGI · ZARGIN AYYUKAN SAƁO · FALALOLI DA LADUBBA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
حسبنا الله ونعم الوكيل Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah