Mabuɗan gaibu biyar ne

Musulunci > Ha > Hadith > Alurani mai girma da ilimansa > Mabuɗan gaibu biyar ne

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Mabuɗan gaibu biyar ne

Bayanin hadisin: Mabuɗan gaibu biyar ne

Gaibu a wajen Allah babu wanda Ya san shi sai Shi, kuma Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mabuɗan gaibu da kuma taskokinsa guda biyar ne: Na farko: Babu wanda ya san yaushe ne alƙiyama zata tsaya sai Allah, nuni ne zuwa ilimummukan lahira, domin ranar alƙiyama ne farkonta, idan sanin mafi kusa ya koru to sanin abin da ke bayansa ma ya koru. Na biyu: Babu wanda ya san yaushe ruwan sama zai zo sai Allah, nuni ne zuwa al'amuran duniyar sama, kuma an keɓanci ruwan sama ne tare da cewa yana da sabubban da suke nunin gudanar al'ada akan afkuwarsa sai dai cewa ba tare da tabbatarwa da kuma yaƙini ba. Na uku; Abin da yake kasancewa a cikin mahaifa; namiji ne ko mace, baƙi ne ko fari, mai cikakken halitta ne ko mai tauyayyar halitta ne, ɗan wuta ne ko ɗan aljanna ne da makamancinsu, kuma an keɓanci mahaifa da ambato dan mafi yawa suna saninta a al'ada, tare da hakan sai ya kore cewa wani ya zama ya san haƙiƙaninsu to waninsu ma shi yafi cancanta. Na huɗu: Babu wanda ya san abin da zai faru gobe sai Allah, nuni ne zuwa nau’ukan zamani da abin da ke cikinsu na abubuwan da zasu faru, kuma an yi amfani da lafazin: "Gobe" dan kasancewar haƙiƙarsa ta zama mafi kusancin zamaninnika, idan ya kasance tare da kusancinsa ba'a sanin abin da zai afku a cikinsa a haƙiƙa, tare da samun alama to abin da ya nisanta shi ne mamafi cancanta. Na biyar: Wata rai bata san a wacce ƙasa zata mutu, nuni ne zuwa wasu al'amuran duniyar ƙasa, tare da cewa al'adar mafi yawancin mutane ita ce ya rasu a garinsa sai dai hakan ba tabbas ba ne, kai da a ce ya rasu a cikin garinsa ba ya sanin a wani guri ne za'a binne shi a cikinsa, ko da ace akwai maƙabartar magabatansa, {Lallai Allah Masani ne Mai bada labari} Mai kewaye sani ne da zahiri da kuma baɗini, da abubuwan da ke ɓoye, da kuma sirrika, sai ayar ta haɗa nau'ikan gaibu, kuma ta gusar da ɓatattun da'awowi.

Koyarwar hadisin: Mabuɗan gaibu biyar ne

Rukunan : ALƘUR'ANI MAI GIRMA DA ILIMANSA · TAFSIRIN ALƘUR'ANI · ILIMIN AƘIDA · IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA · Kaɗaita Allah cikin bauta · TAFSIRIN AYOYI

بسم الله الرحمن الرحيم Lar 16 Jumada al-Awwal
الأربعاء 16 جمادى الأولى
أحدب متناقص Cikakken Wata Raguwa Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
الحمد لله Alhamdulillah - Godiya ta tabbata ga Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah