Musulunci > Ha > Hadith > Hadisi da ilimansa > Na horeku da tsoron Allah, da ji da bi, koda bawa ne mutumin Habasha, za ku ga sabani mai…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 2عن العِرْباضِ بن ساريةَ رضي الله عنه قال: قام فينا رسول الله صلى الله عليه وسلم ذات يوم، فوَعَظَنا مَوعظةً بليغةً وَجِلتْ منها القلوبُ، وذَرَفتْ منها العيونُ، فقيل: يا رسول الله، وعظتَنَا موعظةَ مُودِّعٍ فاعهد إلينا بعهد. فقال: «عليكم بتقوى الله، والسمع والطاعة، وإن عبدًا حبشيًّا، وسترون من بعدي اختلافًا شديدًا، فعليكم بسنتي وسنة الخلفاء الراشدين المهديين، عَضُّوا عليها بالنواجِذ، وإياكم والأمور المحدثات، فإن كل بدعة ضلالة».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa sahabbansa wa'azi wa'azi isasshe zukata sun ji tsoro daga gare shi, kuma idanuwa sun zubar da hawaye daga gare shi, Sai suka ce : Ya Manzon Allah ! kai ka ce wannan wa'azin bankwana ne, saboda abinda suka gani ya kai matukarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wa'azi, sai suka nemi wata wasiyyar dan su yi riko da ita a bayansa, Ya ce: Ina yi muku wasicci da tsoron Allah - Mai girma da daukaka -, hakan da aikata wajibai da barin abubuwan da aka haramta, da ji da bi, wato: Ga shugabanni, koda bawa ne ya shugabanceku ko ya yi rinjaye a kanku, wato ya zama mafi kaskantar halitta sarki akanku kada ku hanu daga hakan, ku bi shi dan tsoron tada fitintinu, domin shi wanda ya rayu daga cikinku zai ga sabani mai yawa. Sannan ya bayyana musu mafita daga wannan sabanin, hakan dayin riko da sunnarsa da sunnar Halifofi shiryayyu a bayansa, Abu bakar Al-Siddik, da Umar Dan Al-khaddab, da Usman Dan Affan, da Aliyu Dan Abu Dalib - Allah Ya yarda su baki daya -, da riketa da turamen hakora wato - turamen hakora na karshe -: Yana nufi da hakan kokari a lazimtar sunna da yin riko da ita, ya kuma gargadesu daga fararrun al'amura kirkirarru a Addini, domin cewa kowacce bidi'a bata ce.
Rukunan : FALALAR SAHABBAI · HADISI DA ILIMANSA · FALALOLI · FALALOLIN SAHABBAI ALLAH YA YARDA DA SU · ILIMIN AƘIDA · SIYASA A SHARI'ANCE · HAƘƘIN SHUGABA A KAN MABIYA · BINCIKE-BINCIKE GAMAMMU CIKIN SUNNA · FALALOLI DA LADUBBA · MUHIMMANCIN SUNNA DA MATSAYINTA · DA'AWA DA HISBA · Merits of the Rightly Guided Caliphs · SAHABBAI