((Ku nisanci abubuwa bakwai masu halakarwa

Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > ((Ku nisanci abubuwa bakwai masu halakarwa

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: ((Ku nisanci abubuwa bakwai masu halakarwa

عن أبي هريرة رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «اجْتَنِبُوا السَّبْعَ الْمُوبِقَاتِ»، قَالُوا: يَا رَسُولَ اللهِ وَمَا هُنَّ؟ قَالَ: «الشِّرْكُ بِاللهِ، وَالسِّحْرُ، وَقَتْلُ النَّفْسِ الَّتِي حَرَّمَ اللهُ إِلَّا بِالْحَقِّ، وَأَكْلُ الرِّبَا، وَأَكْلُ مَالِ الْيَتِيمِ، وَالتَّوَلِّي يَوْمَ الزَّحْفِ، وَقَذْفُ الْمُحْصَنَاتِ الْمُؤْمِنَاتِ الْغَافِلَاتِ».

Bayanin hadisin: ((Ku nisanci abubuwa bakwai masu halakarwa

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana umartar al'ummarsa da nisantar laifuka da sabo guda bakwai masu halakarwa, yayin da aka tambaye shi game da su wadanne ne su? sai ya bayyana su da cewa su ne:

Na farko: Shirka da Allah, ta hanyar rikon kishiya da tamka gare Shi - tsarki ya tabbatar maSa - daga dukkanin wani zance da ya kasance, da kuma juyar da kowace irin ibada daga ibadu ga wanin Allah - Madaukakin sarki - kuma ya fara da shirka; domin cewa ita ce mafi girman zunubai.

Na biyu: Sihiri - shi ne wani na daga kullace-kullace da wasu magunguna da hayake-hayake -, yanayin tasiri a cikin jikin wanda aka yi wa sihirin ta hanyar kisa ko rashin lafiya, ko ya raba tsakanin ma'aurata biyu, shi aiki ne na Shaidan, kuma da yawa daga gare shi ba'a kaiwa zuwa gareshi sai ta hanyar shirka da neman kusanci zuwa ga munanan ayyuka da wani abin da suke so.

Na uku: Kashe ran da Allah Ya hana kashe ta ba da wani abinda ya halatta a shari'ance wanda shugaba zai zartar dashi.

Na hudu: Amfani da riba ta hanyar ci ko waninsa ta fuskokin amfani.

Na biyar: Barna akan dukiyar karamin yaron da babansa ya mutu alhali shi bai kai shekarun balaga ba.

Na shida: Guduwa daga yaki da ake yi da kafirai.

Na bakwai: Tuhumar 'ya'ya mata kamammu da zina, haka nan ma tuhumar maza.

Koyarwar hadisin: ((Ku nisanci abubuwa bakwai masu halakarwa

Rukunan : FIƘHUN HALAYE · ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI · HALAYE ABIN ZARGI · ZARGIN AYYUKAN SAƁO · FALALOLI DA LADUBBA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
الله أكبر Allah Shi ne Mafi Girma

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah