Za'a kirga a binda suka ha'inceka suka saba maka suka yi maka karya, da kuma ukubar da ka …

Musulunci > Ha > Hadith > Alurani mai girma da ilimansa > Za'a kirga a binda suka ha'inceka suka saba maka suka yi maka karya, da kuma ukubar da ka …

Wanda ya ruwaito hadisin: Tirmizi ne ya ruwaito shi

Mai Rauni ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Za'a kirga a binda suka ha'inceka suka saba maka suka y…

Bayanin hadisin: Za'a kirga a binda suka ha'inceka suka saba maka suka y…

Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana karar halin bayinsa, cewa su suna yi masa karya a labari, suna ha'intarsa a amana, suna yin algus a mu'amala, suna saba masa a al'amari, shi kuma yana zaginsu yana dukansu dan ladabtar da su, sai ya tambaye shi game da halinsa ranar Alkiyama tare da su? sai tsira da aminci su tabbata agare shi ya ce: Za'a lissafa abinda suka ha'inceka suka saba maka suka yi maka karya, kuma za'a lissafta ukubarka garesu, idan gwargwadan ukubar ta yi daidai da laifukansu to ba ka da komai, kuma babu komai a kanka, idan kuma gwargwadan ukubarka garesu kasa da laifukansu ne, ya zama falala da kari gareka a lada, idan ukubarka garesu sama da laifukansu ne za’a yi maka ukuba, za'a karbi gwargwadan karin daga gareka za'a ba su, sai mutumin yadan yi nisa ya fara kuka muryarsa tana sama, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce masa: Shin ba ka karanta littafin Allah ba; {zamu sanya ma'auni na adalci ga ranar Alkiyama ba za’a zalinci wata rai wani abuba, idan ya kasance kwatankwacin kwayar komayya ne zamu zo da ita, mun isa zama masu hisabi] [Al-Anbiya;47], ba za’a zalinci wani mutum wani abu ba ranar Alkiyama, kuma ma'aunai za su zama a tsakanin mutane da adalci, sai mutumin ya ce: Wallahi ya manzon Allah, ban ji komai game da ni da su ba sama da na rabu dasu da barinsu, ina shaida maka cewa su 'ya'ya ne sabo da Allah gaba dayansu; dan tsoron hisabi da azaba.

Koyarwar hadisin: Za'a kirga a binda suka ha'inceka suka saba maka suka y…

Rukunan : ALƘUR'ANI MAI GIRMA DA ILIMANSA · TAFSIRIN ALƘUR'ANI · ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI · ILIMIN AƘIDA · TSARKAKE ZUKATA · FALALOLI DA LADUBBA · Imani da Ranar Lahira · TAFSIRIN AYOYI

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
حسبنا الله ونعم الوكيل Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah