Mafificin yinin da rana ta ɓullo a cikinsa yinin Juma'a

Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Mafificin yinin da rana ta ɓullo a cikinsa yinin Juma'a

Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Mafificin yinin da rana ta ɓullo a cikinsa yinin Juma'a

Bayanin hadisin: Mafificin yinin da rana ta ɓullo a cikinsa yinin Juma'a

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa mafificin yinin da rana ta ɓullo a ciknsa shi ne yinin Juma'a. Daga abinda (ginin Juma’a) ya keɓa ta da shi: Allah Ya halicci (Annabi) Adam - aminci ya tabbata agare shi - a cikinsa, a cikinsa ne aka shigar da shi aljanna, a cikinsa ne aka fitar da shi daga aljannar, kuma aka sakko da shi ƙasa, Alkiyama ba za ta tashiba sai a yinin Juma'a.

Koyarwar hadisin: Mafificin yinin da rana ta ɓullo a cikinsa yinin Juma'a

Rukunan : ILIMIN AƘIDA · Imani da Manzanni · ANNABAWA DA MANZANNI MAGABATA AMINCI A GARESU

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
سبحان الله وبحمده Tsarkin Allah da godiyarSa

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah