Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Wanda ya mutu ba ya taranya wani abu da Allah zai shiga Aljanna, wanda ya mutu yana tarany…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عَنْ جَابِرٍ رضي الله عنه قَالَ: أَتَى النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رَجُلٌ فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللهِ، مَا الْمُوجِبَتَانِ؟ فَقَالَ: «مَنْ مَاتَ لَا يُشْرِكُ بِاللهِ شَيْئًا دَخَلَ الْجَنَّةَ، وَمَنْ مَاتَ يُشْرِكُ بِاللهِ شَيْئًا دَخَلَ النَّارَ»
Wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da dabi'u biyu: Wacce take wajabta shiga Aljanna, da wacce take wajabta shiga wuta? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya amsa masa: Cewa dabi'ar da take wajabta Aljanna ita ce mutum ya mutu alhali yana bautawa Allah Shi kadai ba ya taranya wani abu da shi, Kuma cewa dabi'ar da take wajabta wuta ita ce mutum ya mutu alhali shi yana taranya wani abu da Allah, sai ya sanya kishiya ga Allah da tamka a cikin AllantakarSa ko a kasancewar shi ne Mahalicci ko sunayenSa da siffofinSa.
Rukunan : FALALOLI · FALALOLIN TAUHIDI · ILIMIN AƘIDA · FALALOLI DA LADUBBA · IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA · Kaɗaita Allah cikin bauta