Za’a zo da mtuwa kamar siffar farin rago da sirkin baki

Musulunci > Ha > Hadith > Alurani mai girma da ilimansa > Za’a zo da mtuwa kamar siffar farin rago da sirkin baki

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Za’a zo da mtuwa kamar siffar farin rago da sirkin bak…

عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الخُدْرِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «يُؤْتَى بِالْمَوْتِ كَهَيْئَةِ كَبْشٍ أَمْلَحَ، فَيُنَادِي مُنَادٍ: يَا أَهْلَ الجَنَّةِ، فَيَشْرَئِبُّونَ وَيَنْظُرُونَ، فَيَقُولُ: هَلْ تَعْرِفُونَ هَذَا؟ فَيَقُولُونَ: نَعَمْ، هَذَا المَوْتُ، وَكُلُّهُمْ قَدْ رَآهُ، ثُمَّ يُنَادِي: يَا أَهْلَ النَّارِ، فَيَشْرَئِبُّونَ وَيَنْظُرُونَ، فَيَقُولُ: وهَلْ تَعْرِفُونَ هَذَا؟ فَيَقُولُونَ: نَعَمْ، هَذَا المَوْتُ، وَكُلُّهُمْ قَدْ رَآهُ، فَيُذْبَحُ ثُمَّ يَقُولُ: يَا أَهْلَ الجَنَّةِ خُلُودٌ فَلاَ مَوْتَ، وَيَا أَهْلَ النَّارِ خُلُودٌ فَلاَ مَوْتَ، ثُمَّ قَرَأَ: {وَأَنْذِرْهُمْ يَوْمَ الحَسْرَةِ إِذْ قُضِيَ الأَمْرُ وَهُمْ فِي غَفْلَةٍ} [مريم: 39]، وَهَؤُلاَءِ فِي غَفْلَةٍ أَهْلُ الدُّنْيَا {وَهُمْ لاَ يُؤْمِنُونَ} [مريم: 39]».

Bayanin hadisin: Za’a zo da mtuwa kamar siffar farin rago da sirkin bak…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa Za’a zo da mutuwa ranar Alkiyama, kamar siffar namijin tinkiya a jikinsa akwai fari da baki, Sai a yi kira: Ya ku 'yan Aljanna! sai su dago wuyan su da kawunansu suna dubawa. Sai ya ce da su: Shin kun san wannan?. Sai su ce: Eh, wannan mutuwa ce, kuma dukkaninsu hakika sun ganta sun kuma santa, Sannan mai kira ya yi kira: Ya ku 'yan wuta, sai su dago wuyansu su dago kawunansu suna dubawa. Sai ya ce: Shin kun san wannan?. Sai su ce: Eh, wannan mutuwa ce, kuma dukkaninsu hakika sun gan ta. Sai a yankata, sannan mai kira ya ce: Ya ku 'yan Aljanna wanzuwa har abada babu mutuwa,m. Ya ku 'yan wuta wanzuwa har abada babu mutuwa. Wannan dan ya zama kari a cikin ni'imar muminai, da masifa a cikin azabar kafirai. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karanta: {Kuma ka yi musu gargadi da ranar nadama a lokacin da aka hukunta al’amari alhalin kuwa suna a cikin rafkana, kuma ba su yin imani ba.} Ranar Alkiyama za'a rabe tsakanin 'yan Aljanna da 'yan wuta, kuma kowanne zai shiga inda zai dawwama a cikinsa. Sai mai munanawa ya yi nadama dan bai kyautata ba, mai takaitawa kuma dan bai kara alheri ba.

Koyarwar hadisin: Za’a zo da mtuwa kamar siffar farin rago da sirkin bak…

Rukunan : ALƘUR'ANI MAI GIRMA DA ILIMANSA · TAFSIRIN ALƘUR'ANI · ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI · ILIMIN AƘIDA · SIFFOFIN ALJANNA DA WUTA · FALALOLI DA LADUBBA · Imani da Ranar Lahira · TAFSIRIN AYOYI

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
الله أكبر Allah Shi ne Mafi Girma

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah