Kara Ruku'u 533 na Alkur'ani

Ruku'u 533 daga Surah Ash-Shams ne (ayoyi 1 zuwa 15). Yana ɗauke da ayoyi 15 kuma yana cikin Juz 30.

الشمس · Juz 30
Kewaya
Alamomi
Shafi 595
Na gabata Ruku'u 533 Na gaba
سورة الشمس
Juz / Hizb
Juz 30 65.8% (371/564)
Hizb 60 33.0% (95/288)
91:1

وَٱلشَّمْسِ وَضُحَىٰهَا ﴿1﴾

Ina rantsuwa da rãnã da hantsinta.

91:2

وَٱلْقَمَرِ إِذَا تَلَىٰهَا ﴿2﴾

Kuma da wata idan ya bi ta.

91:3

وَٱلنَّهَارِ إِذَا جَلَّىٰهَا ﴿3﴾

Da yini a lõkacin da ya bayyana ta.

91:4

وَٱلَّيْلِ إِذَا يَغْشَىٰهَا ﴿4﴾

Da dare a lõkacin da ya ke rufe ta.

91:5

وَٱلسَّمَآءِ وَمَا بَنَىٰهَا ﴿5﴾

Da sama da abin da ya gina ta.

91:6

وَٱلْأَرْضِ وَمَا طَحَىٰهَا ﴿6﴾

Da ƙasã da abin da ya shimfiɗa ta.

91:7

وَنَفْسٍۢ وَمَا سَوَّىٰهَا ﴿7﴾

Da rai da abin da ya daidaita shi.

91:8

فَأَلْهَمَهَا فُجُورَهَا وَتَقْوَىٰهَا ﴿8﴾

Sa'an nan ya sanar da shi fãjircinsa da shiryuwarsa.

91:9

قَدْ أَفْلَحَ مَن زَكَّىٰهَا ﴿9﴾

Lalle ne wanda ya tsarkake shi (rai) ya sãmi babban rabo.

91:10

وَقَدْ خَابَ مَن دَسَّىٰهَا ﴿10﴾

Kuma lalle ne wanda ya turbuɗe shi (da laifi) ya tãɓe.

91:11

كَذَّبَتْ ثَمُودُ بِطَغْوَىٰهَآ ﴿11﴾

Samũdãwa sun ƙaryata (Annabinsu), dõmin girman kansu.

91:12

إِذِ ٱنۢبَعَثَ أَشْقَىٰهَا ﴿12﴾

A lõkacin da mafi shaƙãwarsu ya tafi (wurin sõke rãkumar sãlihu).

91:13

فَقَالَ لَهُمْ رَسُولُ ٱللَّهِ نَاقَةَ ٱللَّهِ وَسُقْيَـٰهَا ﴿13﴾

Sai Manzon Allah ya gaya musu cewa: "Ina tsõratar da ku ga rãƙumar Allah da ruwan shanta!"

91:14

فَكَذَّبُوهُ فَعَقَرُوهَا فَدَمْدَمَ عَلَيْهِمْ رَبُّهُم بِذَنۢبِهِمْ فَسَوَّىٰهَا ﴿14﴾

Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan suka sõke ta. Sabõda haka Ubangijinsu Ya darkãke su, sabõda zunubinsu. Sa'an nan Ya daidaita ta (azãbar ga mai laifi da maras laifi).

91:15

وَلَا يَخَافُ عُقْبَـٰهَا ﴿15﴾

Kuma bã ya tsõron ãƙibarta (ita halakãwar).

An sabunta a 28 Oktoba 2026 00h24

Ruku 533 a cikin Alkur'ani

15
ayoyi
1
Surah
30
Juz
v.1 – v.15
Ayoyi

Surori a cikin Ruku 533