Abubakar Mahmoud Gumi
Surah Al-Qiyama (القيامة) ita ce surah na Makka ta Alkur'ani tana da ayoyi 40. Ku karanta, ku saurari kuma ku hadda wannan surah tare da kayanmu masu hulɗa.
An sabunta a 10 Yuli 2026 03h52
📖 Karatu minti 2coran.read_full_page : Kara Surah Al-Qiyama →
كَلَّا بَلْ تُحِبُّونَ ٱلْعَاجِلَةَ ﴿٢٠﴾
A'aha! Bã haka ba kunã son mai gaugawar nan (duniya) ne.
وَتَذَرُونَ ٱلْـَٔاخِرَةَ ﴿٢١﴾
Kunã barin ta ƙarshen (Lãhira).
وُجُوهٌۭ يَوْمَئِذٍۢ نَّاضِرَةٌ ﴿٢٢﴾
Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu annuri ne.
إِلَىٰ رَبِّهَا نَاظِرَةٌۭ ﴿٢٣﴾
Zuwa ga Ubangijinsu mãsu kallo ne.
وَوُجُوهٌۭ يَوْمَئِذٍۭ بَاسِرَةٌۭ ﴿٢٤﴾
Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu gintsẽwa ne.
تَظُنُّ أَن يُفْعَلَ بِهَا فَاقِرَةٌۭ ﴿٢٥﴾
Sunã zaton a sako musu masĩfa mai karya tsatso.
كَلَّآ إِذَا بَلَغَتِ ٱلتَّرَاقِىَ ﴿٢٦﴾
A'aha! Iadan (rai) ya kai ga karankarmai.
وَقِيلَ مَنْ ۜ رَاقٍۢ ﴿٢٧﴾
kuma aka ce: "Wãne ne mai tawada?"
وَظَنَّ أَنَّهُ ٱلْفِرَاقُ ﴿٢٨﴾
Kuma ya tabbata cẽwa rabuwa dai ce.
وَٱلْتَفَّتِ ٱلسَّاقُ بِٱلسَّاقِ ﴿٢٩﴾
Kuma ƙwabri ya lauye da wani ƙwabri.
إِلَىٰ رَبِّكَ يَوْمَئِذٍ ٱلْمَسَاقُ ﴿٣٠﴾
Zuwa ga Ubangijinka, a rãnar nan, magargaɗa take.
فَلَا صَدَّقَ وَلَا صَلَّىٰ ﴿٣١﴾
To, bai gaskatã ba, kuma bai yi salla ba!
وَلَـٰكِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ ﴿٣٢﴾
Amma dai ya ƙaryata, kuma ya jũya baya!
ثُمَّ ذَهَبَ إِلَىٰٓ أَهْلِهِۦ يَتَمَطَّىٰٓ ﴿٣٣﴾
Sa'an nan, ya tafi zuwa ga mutãnensa, yana tãƙama.
أَوْلَىٰ لَكَ فَأَوْلَىٰ ﴿٣٤﴾
Halaka tã tabbata a gare ka, sa'an nan ita ce mafi dãcewa.
ثُمَّ أَوْلَىٰ لَكَ فَأَوْلَىٰٓ ﴿٣٥﴾
Sa'an nan, wata halaka tã tabbata a gare ka dõmin tã fi dãce wa.
أَيَحْسَبُ ٱلْإِنسَـٰنُ أَن يُتْرَكَ سُدًى ﴿٣٦﴾
Shin, mutum nã zaton a bar shi sagaga (wãto bãbu nufin kõme game da shi)?
أَلَمْ يَكُ نُطْفَةًۭ مِّن مَّنِىٍّۢ يُمْنَىٰ ﴿٣٧﴾
Bai kasance iɗgo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa (a cikin mahaifa)
ثُمَّ كَانَ عَلَقَةًۭ فَخَلَقَ فَسَوَّىٰ ﴿٣٨﴾
Sa'an nan, ya zama gudan jini, sa'an nan Allah Ya halitta shi, sa'an nan Ya daidaita gaɓõɓinsa;
فَجَعَلَ مِنْهُ ٱلزَّوْجَيْنِ ٱلذَّكَرَ وَٱلْأُنثَىٰٓ ﴿٣٩﴾
Sa'an nan, Ya sanya daga gare shi, nau'i biyu: namiji damace?
أَلَيْسَ ذَٰلِكَ بِقَـٰدِرٍ عَلَىٰٓ أَن يُحْـِۧىَ ٱلْمَوْتَىٰ ﴿٤٠﴾
Ashẽ wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rãyar da matattu?