Kara Ruku'u 542 na Alkur'ani

Ruku'u 542 daga Surah Al-Adiyat ne (ayoyi 1 zuwa 11). Yana ɗauke da ayoyi 11 kuma yana cikin Juz 30.

العاديات · Juz 30
Kewaya
Alamomi
Shafi 599
Na gabata Ruku'u 542 Na gaba
سورة العاديات
Juz / Hizb
Juz 30 84.0% (474/564)
Hizb 60 68.8% (198/288)
100:1

وَٱلْعَـٰدِيَـٰتِ ضَبْحًۭا ﴿1﴾

Ina rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki.

100:2

فَٱلْمُورِيَـٰتِ قَدْحًۭا ﴿2﴾

Mãsu ƙyasta wuta (da kõfatansu a kan duwatsu) ƙyastawa.

100:3

فَٱلْمُغِيرَٰتِ صُبْحًۭا ﴿3﴾

Sa'an nan mãsu yin hari a lokacin asuba.

100:4

فَأَثَرْنَ بِهِۦ نَقْعًۭا ﴿4﴾

Sai su motsar da ƙũra game da shi.

100:5

فَوَسَطْنَ بِهِۦ جَمْعًا ﴿5﴾

Sai su shiga, game da ita (ƙũrar), a tsakãnin jama'ar maƙiya.

100:6

إِنَّ ٱلْإِنسَـٰنَ لِرَبِّهِۦ لَكَنُودٌۭ ﴿6﴾

Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa.

100:7

وَإِنَّهُۥ عَلَىٰ ذَٰلِكَ لَشَهِيدٌۭ ﴿7﴾

Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa dl haka.

100:8

وَإِنَّهُۥ لِحُبِّ ٱلْخَيْرِ لَشَدِيدٌ ﴿8﴾

Kuma 1alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne.

100:9

۞ أَفَلَا يَعْلَمُ إِذَا بُعْثِرَ مَا فِى ٱلْقُبُورِ ﴿9﴾

Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura.

100:10

وَحُصِّلَ مَا فِى ٱلصُّدُورِ ﴿10﴾

Aka bayyana abin da ke cikin zukata.

100:11

إِنَّ رَبَّهُم بِهِمْ يَوْمَئِذٍۢ لَّخَبِيرٌۢ ﴿11﴾

Lalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne?

An sabunta a 28 Oktoba 2026 00h24

Ruku 542 a cikin Alkur'ani

11
ayoyi
1
Surah
30
Juz
v.1 – v.11
Ayoyi

Surori a cikin Ruku 542