Kara Ruku'u 546 na Alkur'ani

Ruku'u 546 daga Surah Al-Humaza ne (ayoyi 1 zuwa 9). Yana ɗauke da ayoyi 9 kuma yana cikin Juz 30.

الهمزة · Juz 30
Kewaya
Alamomi
Shafi 601
Na gabata Ruku'u 546 Na gaba
سورة الهمزة
Juz / Hizb
Juz 30 89.9% (507/564)
Hizb 60 80.2% (231/288)
104:1

وَيْلٌۭ لِّكُلِّ هُمَزَةٍۢ لُّمَزَةٍ ﴿1﴾

Bone ya tabbata ga duk mai nune, mai zunɗe (mai raɗa).

104:2

ٱلَّذِى جَمَعَ مَالًۭا وَعَدَّدَهُۥ ﴿2﴾

Wanda ya tara dũkiya, kuma ya mayar da ita abar tattalinsa.

104:3

يَحْسَبُ أَنَّ مَالَهُۥٓ أَخْلَدَهُۥ ﴿3﴾

Yana zaton cẽwa dũkiyarsa za ta dawwamar da shi.

104:4

كَلَّا ۖ لَيُنۢبَذَنَّ فِى ٱلْحُطَمَةِ ﴿4﴾

A'aha! Lalle ne zã a jẽfa shi a cikin Huɗama.

104:5

وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا ٱلْحُطَمَةُ ﴿5﴾

Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa Huɗama?

104:6

نَارُ ٱللَّهِ ٱلْمُوقَدَةُ ﴿6﴾

Wutar Allah ce wadda ake hurawa.

104:7

ٱلَّتِى تَطَّلِعُ عَلَى ٱلْأَفْـِٔدَةِ ﴿7﴾

Wadda take lẽƙãwa a kan zukata.

104:8

إِنَّهَا عَلَيْهِم مُّؤْصَدَةٌۭ ﴿8﴾

Lalle ne ita abar kullẽwa cea kansu.

104:9

فِى عَمَدٍۢ مُّمَدَّدَةٍۭ ﴿9﴾

A cikin wasu ginshiƙai mĩƙaƙƙu.

An sabunta a 28 Oktoba 2026 00h24

Ruku 546 a cikin Alkur'ani

9
ayoyi
1
Surah
30
Juz
v.1 – v.9
Ayoyi

Surori a cikin Ruku 546